Yau jumma’a a Iran ake gudnarda zaben wakilan majalisar dokokin kasar, zabenda ‘yan hamayya masu rajin canji suka kaurace, yanzu za’a kara ne tsakanin masu ra’ayin rikau wadanda suke goyon bayan shugaba Mahmoud Ahmadinejad, da kuma masu hamayya dashi.
Shugaban addinin kasar Ayatollah Ali khameni yayi kira ga jamma’a su fito sosai, domin ya zama kamar yadda yace ishara ga makiyan Farisa, watau kasashen yammacin duniya wadanda suke yakin ganin ana ci gaba da azawa kasar takunkumin karya tattalin arzki.
Manyan kasashen duniya suna matsa kaimin takunkumi kan Iran da nufin tilastawa kasar ta tsaida shirin nukiliyarta, suna faragbar shirin nata wani kokari ne na kera makaman nukiliya. Iran ta dage shirinta na farar hula ne.
‘Yan takara kalilan ne masu ra’ayin canji cikin mutane dubu uku da dari hudu da suke takarar cike kujeru 290 a majalisar dokokin kasar.