Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana zaben gwamna a jihar Edo Nigeria

A yayinda ake baiyana tsoron barkewar tarzoma da zargin yin magudi, yau Asabar aka yi zaben gwamnan a jihar Edo a can Nigeria. Dukkan jam’iyun dake takara a wannan zabe suna zargin juna da laifi kokarin tada zaune tsaye da sayen kuri’u da kuma kokarin kashe wasu yan siyasa.

Duk da haka wakiliyar Muryar Amirka Heather Murdock ta aiko da rahoton cewa wasu masu zabe suna baiyana fatar za’a gudanar da zaben cikin yanci da adalci.

Masu lura da harkokin siyasar Nigeria sunce wannan zabe zata tantance ko kuma zata yi hasashen abinda zai faru a zaben da za’a yi a Nigeria a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar idan Allah ya kaimu, lokacinda za’a gwada farin jinin jam’iyar PDP wadda take jan ragamar mulkin kasar.

A harabar wata rumfan zabe a kauyen Aduwawa, wasu mutane sun nuna fushinsu akan rashin sunayensu akan rajistan zabe.

Ana takara tsakanin gwamnan Adams Oshiomhole na jam’iyar AC da Janaral Charles Airhiavere mai ritaya na jam’iyar PDP

XS
SM
MD
LG