An bude rumfunan zabe a jihar Carolina ta kudu yau Asabar domin zaben fidda dan takarar shugaban Amurka na jam’iyyar Republican, da ake jin ana kusan kunnen doki tsakanin wadan da suke kan gaba.
Wadan da suke sahun gaba a zaben na yau sun shirya kaddamar da yakin neman zabe a wuri da kuma lokaci guda, a jihar dake kudu maso gabashin Amurka.
Sakamakon kuri’ar neman jin ra’ayoyin jama na baya bayan nan ya nuna tsohon kakakin majalisdar wakilan Amurka Newt Gingrich ya yunkuru sosai yana kalubale ga tsohon gwamnan Massachussetts Mitt Romney.
A jiya jumma’a Romney ya dan tarfa ruwa kan kada a dora tsammani ainun, yana cewa “ai abin yana tsumarwa ganin ana kunnen doki a yanzu haka da ana dab da zabe.”
A makon jiya galibin masu sharhi kan harkokin siyasa sun nuna cewa Mitt Romney zai sami nasara ba tareda wani wahala a jihar ta Carolaina ta kudu.Amma bayan caccakar da abokan hamayya suka yi masa da kuma canji da aka samu cikin masu takararar cikin makon nan, yanzu masu fashin bakin suna ganin tazarar ba zata yi yawa a zaben nan yau.
Sai tayu Gingrich ya amfana da janyewar da Gwamnan Texas Rick perry yayi daga zaben ranar Alhamis kuma ya goyi bayan Newt Gingrich din.
‘Yan takarar Romney da tsohon senata mai wakilatar jihar Pennsylvania Rick Santorum d awakili maj;aisar wakilan Amurka Ron Pual sunyi muhawara ranar Alhamis da ta wuce.