Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yiwa Ma'aikatar Tsaron Amurka Ta Pentagon Kutse


Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, na ci gaba da nuna damuwarsu game da yadda masu kutse da gwamnatoci ke marawa baya suke amfani da kafofin sadarwa irinsu Twitter da Facebook, suna yiwa kwamfutocin ma’aikatar tsaro kutse.

Duk da yake wasu lokuta kuskuren da mutane ke yi na danna wani adireshi ko link da aka aika musu ta email ya fi yawa a kafofin sadarwa, a cewar jami’ai, saboda mutane suna hulda da abokansu ne ta kafofin sadarwa.

A yunkurin farko masu kutsen kasar Rasha suka sami nasarar shiga kwamfutar jami’in ma’aikatar Pentagon. Amma harin bai zo ta hanyar email ba, ko wasu fayil da aka gurbata ba.

A cewar jami’an an kai harin kutsen ne ta kafe wani adireshi da aka saka cikin wani rubutu da aka kafe ta kafar Twitter, wanda ke tallar guraren shakatawa na lokacin bazara masu rahusa, wanda hakan zai iya sa kowanne irin mutum ya danna adireshin.

Yayin da kamfanoni da gwamnatoci a fadin duniya ke horas da ma’aikatansu domin su dinga nazari kafin bude wani link da aka aiko musu ta email, yanzu haka masu kutse sun sami sabuwar hanyar kai hare-hare, inda suke hankoron kafofin sadarwar mutane, da suke ganin mutane ba zasu ankara ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:17 0:00

XS
SM
MD
LG