WASHINGTON DC —
Malam Abubakar Ahmed, ya fadi cewa duk da cewa ana samun wutar lantarki fiye da Da, babar matsalar da yawancin 'yan Najeriya ke fuskanta ita ce yawan kudin wutar. ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen rage kudaden wutar.
Ustaz Ibrahim Damaturu, shi ma ya koka akan wannan matsalar, inda yace ya kamata a duba batun biyan kudi bai daya, wanda talaka bai da halin yin hakan kuma ba ya samun abinda ya ke biya.
A nasa ra'ayin, Kanti Alhaji Uba na Allhaji Barau, kwararre a sha'anin wutar lantarki a Najeriya shi ma ya yi kira ga gwamnati da ta sassauta ta kuma inganta wutar lantarki yadda 'yan kasar zasu sami karfin guywa kuma hakan zai kara kashin bayan tattalin arziki.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, yace zuwa badi idan Allah ya kaimu, Najeriya zata cimma karin kashi arba'in na wutar lantarki ko'ina a cikin kasar. ya kuma ce gwamnati na sane da makudan kudin da ake karba wajen talakawa kuma gwamnatin tarayya zata shigo cikin wannan maganar don daukar mataki.
Tuni 'yan Najeriya ke jinjinawa wannan matakin da gwamnati zata dauka. Ustaz Mohammed Ibrahim Damaturu ya yabawa wannan matakin kuma yayi kira ga talakawa masu amfana da wutar lantarki da su kafa wata kungiya, don a sami fahimta tsakaninta da kamfanonin da ke samar da wutar lantarki.
Ga karin bayani daga Hassan Maina Kaina.