Ganin yadda ake ta korafi kan yadda kungiyar “EUMOA” ta kasashe 8 rainon Faransa masu amfani da takardar kudin CFA ke kasa aiwatar da shawarwarin da su ka yanke, manyan Sakatarorin gwamnatocin kasashen sun shirya taron bita.
Wakilinmu Souley Mummuni Barma ya ce mayan Sakatarorin gwamnatocin sun shirya taron ne a matsayinsu na masu saka ido kan aiwatar da manufofin kungiyar ta EUMOA, musamman game da abin da ya shafi walwala da kuma saukin zirga-zirga tsakanin kasashensu – musamman yadda jami’an tsaron wasu kasashen kan takura ‘yan wasu kasashen kungiyar ta EUMOA.
Abdukarim Lansari, Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren kungiyar, ya ce mutanen kasashen daban-daban bas u da matsala tsakaninsu; matsalar tsakanin matafiya ne da hukumomin kasashen da su ke son shiga – musamman banagern ‘yansanda. Duk da yak e taron na kasashen da ke amfani da harshen Faransanci ne, an gayyaci kasar Gana don jin ra’ayin wasu kasashen.
Ga cikakken rahoton daga Souley Barma: