Jam’iya mai mulki a kasar Ghana ta sanar da sunan sabon shugaban kasar da aka rantsar John Mahama a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar da za a gudanar.
Mr. Mahama zai maye gurbin marigayi shugaba John Atta Mills wanda yake shirin tsayawa takara kafin rasuwarsa ba zato ranar Talata yana da shekaru 68 da haihuwa.
A cikin hirarshi da Muryar Amurka, ministan sadarwa na Fritz Baffour yace shugabannin jam’iyar National Democratic Congress sun bayyana goyon bayan Mr. Mahama yau alhamis. Ana kyautata zaton tabbatar da zabenshi a matsayin dan takarar jam’iyar a wajen babban taron jam’iyar na kasa.
Kawo yanzu, jami’ai basu bayyana cutar da ta kashe shugaba Mills ba, sai dai tsohon shugaban kasar Ghana, Jerry Rawlings ya shaidawa BBC cewa, Mr. Mills ya yi fama da cutar sankara. Ya kuma bayyana cewa, da Mr. Mills ya maida hankali wajen jinyar cutar da ya yi tsawon kwana fiye da haka.