Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Neman Hanyoyin Da Za’a Inganta Makarantun Allo.


Almajiri School
Almajiri School

Wata kungiya mai zaman kanta da hadin gwiwar 'yan jarida na tattaunawa akan hanyoyin da za abi domin inganta makarantun allo a arewacin Nigeria.

Gidauniyar nan da ake kira NEEM ta shirya wani taro na musammam da ‘yan jarida domin musayar ra’ayi akan yadda za a inganta makarantun allo a fadin arewacin Nigeria.

Daya daga cikin burin iyayen yaran nan masu karatu a irin wadanan makarantun shine yaran su haddace Al-kura’ni mai tsarki.

To amma kuma sau tari sai a samu akasin haka, domin sai daliban su rikide su zame wani abu na daban, wata sa’a ma sukan zame barazana ga al’ummar kasa ko kuma su kama barace-barace.

Malam Asharaf Kabiru Usman shine babban Jami’in gidauniyar kuma ya shaidawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari dalilin su na neman tattaunawa da ‘yan jarida kan wannan batu.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG