An yi zaben shugaban kasa a kasar Mali jiya lahadi a cikin tsaro mai tsanani don gudun barkewar rikici inda ake takaddamar baiwa Ibrahim Boubacar Keita mai ci yanzu Karin wa’adin shekarun biyar ko kuma a canza shi da dan adawa Soumalia Cisse.
Ana ci gaba da kirga kuri’u a mazabu 23,000 na fadin kasar bayan da aka rufe runfunan zabe da karfe 6 na yamma.
Keita dan shekara 73 ya samu kashi araba'in da biyu cikin dari na kuri’un da aka jefa a cikin masu nema 24 a zayen farko na zaben, idan aka hada da kashi goma sha takwas cikin dari da Cisse dan shekara ya samu, wanda kuma ya fadi zaben shekara 2013 da Keita ya lashe.
An dauki kwanaki biyar kafin sakamakon zagayen farko na zaben ya fita. sai dai ana kyautata zaton samun sakamakon zagaye na biyu na zabe da wuri, kasancewa 'yan takara duka kwara biyu ne kadai yanzu.
Gwamnati ta kara habbaka tsaro a zaben ranar lahadin inda ta aika da Karin sojoji 6,000 a Karin 30,000 dake da akwai a kasa
Facebook Forum