Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kidayar Zabe a Iraqi


Magoya bayan jam'iyyar Komunis, a Iraqi.
Magoya bayan jam'iyyar Komunis, a Iraqi.

​Jami'an hukumar zaben Iraki sun fara kidaya kuri'u a yau dinnan Alhamis, bayan gudanar da babban zabe a kasar, wanda shi ne na farko tun bayan da sojojin Amurka su ka fice daga kasar a 2011.

Masu rajistar zabe sama da miliyan 20 ne ke da damar kada kuri'a a zaben da aka gudanar ranar Laraba na Majalisar Dokokin Iraki mai kujeru 328.

Duk kuwa da yawan 'yan sandan da aka tura, da kuma hana yawo da motoci a birnin Bagadaza, tashe-tashen hankula masu nasaba da zaben sun yi sanadin mutuwar mutane 12 a sassan kasar.

Jami'an tsaro sun bayyana ciwa bama-baman da aka dana a gefen hanya da kuma jerin kunar bakin wake da aka auna kan masu kada kuri'a da tasoshin zabe a sassan arewaci da yammacin kasar sun yi ta'adi.

Duk kuwa da tashe-tashen hankulan, wasu 'yan Irakin da dama sun kuduri aniyar kada kuri'unsu, ga wasu don fatansu na samin sabuwar gwamnatin da za ta kawo sauye-sauye ga na baya.
XS
SM
MD
LG