An ware kyautar ne musamman ga matasan ‘yan wasa da basu wuce shekaru 21 da haihuwa ba wadanda suke buga wasannin su a nahiyar kasashen Turai. Kuma ‘yan jaridu marubuta labarin wasanni a kasashen nahiyar turai ne suke kada kuri'a yayin zaben.
Dan wasan Felix ya samu kansa cikin jerin sunayen ‘yan wasan ne bisa irin haskakawa da yayi a kungiyarsa ta Benfica, a karkar wasan da ta gabata da kuma wasan da ya buga wa kasar sa Portugal na nahiyar Turai, kafin daga bisani Atletico Madrid ta sayeshi akan kudi yuro miliyon €126.
Matthijs de Ligt shine ya lashe lambar yabo ta karshe a shekarar da ta wuce kuma ya yana cikin jerin ‘yan wasa 20 a wannan shekara.
Ingila tana da wakilai da za'a zaba wada suka hada Jadon Sancho, Mason Mount da kuma Phil Foden, a akwai Matteo Guendouzi na Arsenal sai Moise Kean dan wasan Everton Ga cikekken jerin sunayen yan wasan da kungiyoyin su Matthijs de Ligt ( Juventus) Alphonso Davies ( Bayern Munich) Gianluigi Donnarumma ( AC Milan ) Ansu Fati ( Barcelona) Phil Foden ( Manchester City) Matteo Guendouzi ( Arsenal ) Erling Håland ( Red Bull Salzburg) Kai Havertz ( Bayer Leverkusen ) Joao Felix ( Atletico Madrid ) Dejan Joveljic ( Eintracht Frankfurt ) Moise Kean ( Everton ) Kang-in Lee ( Valencia ) Andriy Lunin ( Real Sociedad ) Danyell Malen ( PSV Eindhoven ) Mason Mount ( Chelsea ) Rodrygo ( Real Madrid ) Jadon Sancho ( Borussia Dortmund ) Vinicius Jr. ( Real Madrid ) Ferran Torres ( Valencia ) Nicolo Zaniolo ( AS Roma