Sakataren watsa labarai na kungiyar,Alhaji Muhammad Magaji ne ya shaida hakan a taron maneama labarai a garin Gombe,ciki harda wakilin muryar Amurka,Abdulwahab Muhammad.
Ya bukaci gwamanatin tarayya dana jihohi dasu bulloda wata dabarar da zai toshe gibin daza a samu a kakar noman bana.
Ya kara da cewa “wannan babban matsalace a halin da ake ciki a kasar na ana zaune lafiya ma yaushe manoma suka samu sukayi noma balle ace babu zaman lafiya,kullum yanda ake fadi in babu zaman lafiya babu abunda za’a iya yi ko addini saboda haka wannan ya shafi noma da kiwon kware,an riga an tarwatsa kauyukansu sun waste, ta inna zasu samu suje noma, saboda haka wanna abun da yake faruwa ya kawo wa noma cikas masammam arewa maso gabas ko shakka babu zai shafi kokarin da akeyi na samar da abinci isashe.”
Yana kuma mai jadada cewa a taimakawa manoma da yankinsu suke zaune lafiya domin su kara yawan abunda suke nomawa saboda cike gibin wadanda ke da matsala.