Mashahurin dan kasuwan nan Sebastian Pinare ake sa ran ya samu nasara a zaben kasar Chile, sai dai kuma ba tabbacin ya samu kashi hamsin na kuriun da ake bukata wanda zai hana aje zagaye na biyu na zaben wanda za a yi a cikin watan gobe.
Pinera dan shekaru 67 yayi kanfe ne da batun rage haraji domin inganta harkokin kasuwanci a kasar domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Mai bi masa a wannan takarar ko shine Sanata Alejandro Guiler tsohon maaikaci talabijin.
Shi kuma yayi nasa kanfe din ne da cewa zaici gaba da manufofin shugaba Michelle Bachelet musammam batun Karin haraji da za a yi anfani dashi wajen biyan kudin da za a inganta harkokin ilmi a cikin kasar dama sauran wasu abubuwan jin dadin jamaa.
Shi dai Bachelet yayi shugabancin kasar daga shekarar 2006 zuwa 2010 lokacin da Pinera ta gaje ta, kuma ga bisa dukkan alamu tarihi zai sake maimata kansa.
Akwai sauuran ‘yan takara 6 dake cikin wannan takarar.
Duka dai a zaben na yau ne masu jefa kuria zasu zabi shugabannin majilisar dokokin kasar.
Facebook Forum