Hukumomin shara’a a Nigeria sun gudanar da wani taro domin samo hanyar magance cin zarafin yara kanana da mata.
Dukkan Kwamishinonin sharia ne na daukacin dukkan jihohin Nigeria ne ke halartan wannan taron.
Da yake wa manema labarai karin haske, Ministan shariar Najeriya Abubakar Malami yace an shirya taron ne don duba rawar da hukumomin sharia ka iya takawa wajen maido da tsaro a kasar, kana kuma da duba hanyoyin magance cin zarafin kananan yara da mata dake neman zama ruwan dare a kasar.
Tun da farko da yake bude taron gwamnan jihar Adamawa Sen. Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya yabawa gwamnatin tarayya bisa kokarin shawo kan matsalar tsaro a shiyar arewa maso gabashin kasar, kana kuma yayi tir da tashe-tashen hankulan da suka auku a wasu sassan kudu maso gabashin Najeriya.
Ga Ibrahim Abdulazeez da karin bayani.
Facebook Forum