Sabbin zanga-zanga sun barke jiya Lahadi a fadin duniyar Musulmi da Larabawa.
Ana boren ne domin nuna rashin amincewa da ayyana Kudus da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi a matsayin babban birnin Isra'ila.
Jami’an tsaron Lebanon sun yi amfani da ruwan zafi da barkonon tsohuwa a wajen ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin Beirut.
Matakin kokari ne na dakatar da ‘yan Lebanon da Falasdinawa masu zanga-zanga wadanda su ka yi ta jifa kan ofishin Jakadancin.
Yayin zanga zangar, masu boren kona wani mutum-mutumin Trump, da tutocin kasashen Amurka da Isra’ila.
A kasar Indonesiya, wadda ta fi yawan Musulmi a duniya, dubban mutane sun yi ta zanga-zanga a harabar ofishin jakadancin na Amurka da ke Jakarda, babban birnin kasar.
Haka kuma an yi zanga-zangar a kasashe irin su Jordan da Turkiyya da Pakistan da Malaysia da Masar da kuma yankin kasar Falasdinu mai makwabtaka da Isra’ila.
Firaministan Isira’ila Benjamin Netanyahu ya yi Allah wadai da abin da ya kira munafurcin wadanda su ka yi suka kan shawarar da Trump ya yanke.
Natanyahu bayyana hakan ne gabanin ya bar kasarsa jiya don ganawa da Shugabannin yankin Turai.
Facebook Forum