Everton tana aiki tare da hukumar da take yaki da nuna wariyar bambanci launin fata, don bincikar wadanda suka rera waka ta wariyar launi ga dan wasanta dan kasar Colombian Yerry Mina.
Kungiyar ta Everton tace tana da masaniyar cewa, an wallafa faifayen Bidiyo na nuna banbanci launi, a shafin sada zumunta na yanar gizon wasu wanda ta nisanta kanta da cewar bata da alaka da kulob din.
A shekara ta 2017 an gargadi magoya bayan Manchester United kan irin wannan munmunar dabi'ar ta wariyar launi fata kan dan wasanta Romelu Lukaku.
Da zaran an kammala bincike wajan gano waddanda suka aikata wannan lamari, hukumar ta yaki da nuna wariya zata tura da rahoto zuwa ga hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Football Association domin hukunta wanda suke da hanu kan lamarin.
Facebook Forum