Ana ci gaba da matsin lambar neman jinkirta wasannin bazara na Olympics da za a yi a Tokyo saboda annobar Coronavirus, yayin da yawan wadanda suka kamu da ita ya haura a Italiya.
Frai ministan Japan Shinzo Abe, ya ce yana da matukar wahala a gudanar da wasannin na Olympics ta hanyar da ya kamata, kuma ‘daga lokacin wasan abu ne da ba za a iya kaucewa ba, idan har ana son kare lafiyar ‘yan wasan.
Jami’an wasannin na kasar Australia sun fadi cewa, “a bayyane ya ke” cewa ba za a iya gudanar da Olympic ba kamar yadda aka tsara a watan Yuli.
Shi kuma kwamitin wasannin na kasar Canada cewa ya yi, ko da za a gudanar da wasan na Tokyo a wannan bazara, ‘yan wasan kasar Canada ba za su je ba.
Kasar dai ta yi kiran da a jinkirta wasannin har na tsawon shekara guda.
Facebook Forum