Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba da Neman Jirgin Karkashin Ruwa da Ya Bace a Gabar Tekun Argentina


Jirgin karkashin ruwanda ya bace da ya kasance mallakar kasar Argentina an kirkirashi ne a kasar Jamus
Jirgin karkashin ruwanda ya bace da ya kasance mallakar kasar Argentina an kirkirashi ne a kasar Jamus

Tun ranar Larabar da ta gabata ne jirgin karkashin ruwa kirar Jamus ya bace kuma yanayi mara kyau na kawowa jiragen ruwa da na sama daga wasu kasashe dake taimakawa wurin ceto jirgin dake dauke da mutane 44 cikas

Rukunonin jiragen ruwa da jiragen sama na kasashe daban-daban, na ta daure ma matsalar igiyoyin ruwa da kan haura da tsawon mita 8, da kuma iska mai gudun kilomita 74 a sa’a guda, a kokarin su na neman jirgin karkashin ruwa mai dauke da mutane 44 mallakin kasar Argentina.

Jirgin karkashin ruwan, kirar Jamus, mai aiki da karfin lantarki da man diesel, mai kuma nauyin ton 2000 da tsawon mita 66, ya bace ne tun ranar Laraba daga nisan kilomita 430 daga gabar tekun Argentina. Jirgin, mai suna San Juan (Huwan), ya fara aiki ne tun a shekarar 1985. Mace ta farko da ta zama jami’ar jirgin karkashin ruwa na Argentina, Eliana Krawczyk na cikin wadanda ke cikin jirgin.

Jiragen ruwa na soji da na bincike daga kasashen Brazil da Amurka da Chile da Uruguay da kuma Burtaniya sun shiga wannan binciken. Amurka ta tura da jirgin bincike na NASA, mai iya hango jirgin karkashin ruwa da kuma tawagar masu ayyukan ceto na hadarin jirgin karkashin ruwa.

An ce Paparoma Farncis, wanda dan asalin kasar ta Argentina ne, na kan addu’a wurjanjan saboda wadanda ke cikin jrgin su dawo lafiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG