A ranar Laraba 8 ga watan Yuli ne Ministan ilimin kasar Adamu Adamu ya sanar da matsayar gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa kasar. Hakan dai ya sanya daliban Najeriya ne kadai ba za su rubuta jarabawar kammala sakandare ba da hukumar kula da jarabawar makarantun sakandare ta Afrika ta yamma ke shiryawa a kowace shekara.
Sanarwar gwamnatin Najeriya ta baya-baya ta ci karo da bayanan da ma’aikatar ilimin kasar ta fitar da ke nuna sake bude makarantun kasar a karshen watan Yuli zuwa kwanakin farko na watan Agusta.
Malam Abdullahi Getso, ya yi tsokaci game da wannan batu a yayin kudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin Juma’a na Sahaba da ke Kano ya na mai cewa ya kamata a bar yara su koma makaranta don su ci gaba da koyon tarbiyya.
Sai dai Comrade Yahaya Shu’aibu Ungogo, wani mai sharhi kan lamuran ilimi a Najeriya na cewa ba abinda ya fi rayuwar bil'adama muhimmanci, don haka ba kuskure ba ne a hana rubuta wata jarabawa ko komawa makaranta saboda daukar matakai a makarantu zai zama da wahala ganin yadda wasu ke watsi da dokokin da aka sanya don dakile yaduwar cutar coronavirus.
Makomar tarbiyyar yara na daga cikin al’amuran da wasu ke dubawa game da ci gaba da kasancewar makarantu a rufe. Malam Muhammad Mustafa Dandume, Malamin tarbiyya ne a Kano, ya ce da a bude kasuwa ko masallaci gara a bude makarantu saboda shugabanni da malaman makaranta za su iya tsara yadda za a kiyaye matakai tunda sun san adadin dalibansu. Ci gaba da kasancewar daliban a gida na iya tarwatsa tarbiyyarsu a cewarsa.
Masu kula da lamura dai na ganin akwai bukatar hukumomi a Najeriya su lalubo hanyoyin koyar da dalibai darrussa a yayin da gwamnati ke kokarin kawar da cutar coronavirus.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Kwari.
Facebook Forum