Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Ce-ce-kuce Akan Dokar Hana Zirga-zirga A Najeria


A yayin da adadin masu dauke da cutar coronavirus ya ke karuwa a Najeriya, yanzu haka dai gwamnatin kasar ta ce ba za ta yi gaggawar dage dokar hana yawo nan take ba, wajibi ne ta yi taka tsan-tsan da bazuwar cutar a tsakanin al’umma.

Wannan mataki da gwamnatin ta dauka ya zo ne a dai-dai lokacin da yawan masu dauke da cutar ta COVID-19 ya kai 6,175. Kawo yanzu, Jihar Legas da ita ce cibiyar kasuwancin Najeriya, tana kan gaba da mutane 2,624 da suka kamu da cutar, sai jihar Kano wadda ita ce cibiyar kasuwancin Arewacin kasar ta ke da mutane 842 da suka kamu da cutar.

Matakin hana zirga-zirga tsakanin jama'a tare da rufe guraren kasuwanci ya haifar da koma baya ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa, da harkokin addinai, musanman a wannan wata na azumin Ramadan.

Wasu daga cikin mazauna yankunan sun bayyana takaicin yadda harkokin kasuwancinsu suka tsaya cik, tare da kira ga gwamnati da ta kara sassautawa. Wasu kuma suna zargin makarkashiya ce kawai ga addinai a duniya ta hanyar hana ibadah a gurare da dama.

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harakokin addinin Musulunci a Najeriya Muhammad Sa'ad Abubakar ya ce za'a gudanar da sallar Idin bana ne a masallatan Juma'a maimako a fakon idi domin kaucewa yawan cunkoso.

Wani malamin addinin Islama Dr. Bashir Yankuzo ya ce, babu laifi idan an dauki wannan mataki domin rigakafi da kare lafiyar jama'a, abu ne da musulunci ya yarda da shi.

Yanzu haka dai gwamnatin Najeriya ta kara wa’adin hana zirga-zirga da hada-hada na makwanni biyu, duk dai a kokarin magance wannan matsala ta annobar coronavirus.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Babangida jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG