An dade ana cece-ku-ce game da batun kirkiro ‘yan sandan jihohi ko kuma na yanki a Najeriya amma haka ba ta cimma ruwa ba sai a wannan karon da gwamnatin Shugaba Buhari ta kudiri aniyar kaddamar da shirin ‘yan sintirin yanki da ke kama da ‘yan sandan yanki, kamar yadda ya ke a wasu kasashe. Wasu na gani daukar wannan mataki a yanzu bai rasa nasaba da tabarbarewar lamurran tsaro a Najeriya.
Tuni dai wasu gwamnoni suka yi amannar cewa zasu taimaka.
Gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Isiyaku, a wani taron harkokin tsaro da sarakunan gargajiya a jihar, ya ce su a shirye suke su tabbatar da dorewar shirin.
To sai dai kuma, wannan saurin amincewar da gwamnonin suka yi ya soma kawo shakku a zukatan wasu. Ambasada Hassan Jika Ardo, jakadan Najeriya a yankin Karebiya, ya ce akwai abun lura musamman ma ga wasu gwamnonin Najeriya.
Shi ma wani tsohon jami'in tsaro ASP Yakubu Sule, ya ce akwai wani hanzarin da ba gudu ba muddin aka ce jihohi ne zasu kula da ragamar shirin na ‘yan sandan yankuna.
Don tabbatar da kaddamar da shirin rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafa kwamitoci game da shirin biyo bayan sahalewar da Shugaba Buhari ya yi.
DSP Suleiman Yahya Nguroje, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ya yi karin haske akan abinda ake nufi da ‘yan sandan yanki, wato Community Policing. Yanzu dai abinda talaka ke fata shine Allah ya kawo tsaro ko a daina jin tsoro.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum