Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ce-Ce-Ku-Ce Kan Yadda Ruwan Sama Ya Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Najeriya


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate).
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate).

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriyar da ke tafka muhara a kafafen sada zumunta, sun kwatanta wannan al’amari a matsayin abin kunya ga kasar yayin da shugabannin majalisar ke cewa ba laifinsu ba ne.

Muhawara ta kaure a Najeriya, bayan da ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya ya haifar da malalar ruwa a cikin ginin majalisar dokokin kasar.

Wasu hotuna da bidiyo da aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta dauke da wasu daga cikin ma’aikatan majalisar suna kwarfe ruwan suna zubawa a bukatai, sun sa ‘yan Najeriya suna ta tsokaci tare da dasa alamar tambaya kan ina ake kai kudaden da ake warewa ginin don a rika yi masa kwaskwarima.

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriyar da ke tafka muhara a kafafen sada zumunta, sun kwatanta wannan al’amari a matsayin abin kunya ga kasar yayin da shugabannin majalisar ke cewa ba laifinsu ba ne.

Yadda ma'aikata suka yi ta hidimar kwarfe ruwan da ya taru a majalisar (Facebook/ Channels TV)
Yadda ma'aikata suka yi ta hidimar kwarfe ruwan da ya taru a majalisar (Facebook/ Channels TV)

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata bayan da aka yi ruwan sama mai karfin gaske a birnin na Abuja.

Hakan ya sa rufin ginin ya fara digar da ruwa har ta kai ga ya malala a dakin farko na shiga cikin ginin.

“Ina duk kudaden da ake warewa don yin gyara a ginin majalisar dokokin.” Official_aadex ya tambaya a shafin Instagram.

“Damuwowi sun yi yawa a kasar nan.” In ji amycocoo.

Karin bayani akan: Janar Sani Abacha, Dattawa Ahmad Lawan, Sanata Sabi Abdullahi, majalisar dokokin, Shugaba Muhammadu Buhari, Abuja, Nigeria, da Najeriya.

Rahotannin sun ce naira biliyan 37 aka ware a kasafin kudin 2020 don yin gyara a ginin majalisar wanda ke dauke da zauren majalisar wakilai da na dattawa, abin da shugabannin majalisar suka musanta.

“Amma abin kunya ne saboda irin kudin da ake warewa na gyaran majalisar, bai kamata haka ta faru ba.” Wani dan Najeriya, Alhaji Yaro Bulbula ya fada a tsokacin da ya yi a labarin da Aminiya ta wallafa.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan (Facebook/ Nigerian Senate)
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan (Facebook/ Nigerian Senate)

Sai dai shugabannin majalisar dokokin, sun fito sun kare kansu dangane da wannan lamari, inda suka ce ba laifinsu ba ne da ginin ya tsinci kansa a cikin wannan yanayi.

Shugaban majalisar Dattawa Ahmad Lawan, yayin zaman da aka yi a ranar Laraba, ya ce sun kai wa shugaban kasa koke kan bukatar a yi wa ginin kwaskwarima.

“Kowa ya san cewa lokaci ya yi da za a yi wannan ginin kwaskwarima, mun je mun sami shugaban kasa, ya kuma tura ma wajen hukumar da ke kula da birnin tarayya FCTA.

“Kudin da aka ware na biliyan 37 ba kasafin majalisar ba ne, kudi ne da hukumar FCDA ta ware.” In ji Lawan kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito a lokacin da Sanata Sabi Abdullahi ya bijiro da batun a zaman majalisar.

A cewar Sabi, wanda shi ne mai tsawatarwa a zauren majalisar Dattawa, an warewa ginin naira biliyan 37 bayan da shugabannin majalisar suka gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Instagram/speakergbaja)
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Instagram/speakergbaja)

“Amma a lokacin da annobar COVID-19 ta barke, an rage kudin zuwa biliyan 9, da niyyar za a rika gyaran daki-daki, amma har yanzu ba abin da aka yi.”

Hukumar ta FCDA ba ta ce uffan ba dangane da wannan al'amari.

An dai kammala ginin na majalisar dokokin Najeriyar ne a shekarar 1999 bayan da aka fara shi a shekarar 1996 a zamanin mulki soja na gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Bincike ya nuna cewa naira biliyan 7 aka kashe wajen gina majalisar wacce kamfanin ITB Nigeria ya gina.

XS
SM
MD
LG