Tarar dai ta raba kan Majalisar gudanarwa da Hukumar kula da Kafafen Yada Labarai ta kasa.
Tsohon Ministan Watsa Labarai kuma Shugaban Majalisar gudanarwa ta Hukumar Kula da Kafafen yada Labarai Ikra Aliyu Bilbis, ya ce wannan doka ba ta dace ba.
Ya zargi Ministan Watsa labarai da Al'adu Lai Mohammed akan cewa shi kadai ya zauna ya tsara dokar ba tare da tuntubar Majalisa ba.
A lokacin da ya ke bayyana ra'ayinsa kan wannan batun, Sakataren Kungiyar 'yan Jaridu ta kasa Shuaibu Leman ya ce dokar ba ta yi ba saboda ba a tuntubi masu ruwa da tsaki ba.
Hakan ya sa yake ganin soke dokar a yanzu shi ne mafi a'ala ga kasa.
Shi Kuwa Malami a Jami'ar Jihar Nasarawa kuma mai fashin baki a al'amuran yada labarai Auwalu Salihu yana gani dokar ba ta samu goyon bayan al'umma ba musamman wadanda ke da alaka da kafafen yada labarai saboda haka barin yin amfani da dokar ko kuma a sake yi mata gyara zai fi.
Amma ga Ministan Watsa Labarai da Al'adu na kasa kuma Madugun gudanar da dokar Alhaji Lai Mohammed ya ce an yi dokar ne domin kare mutunci kasa.
A yanzu dai 'yan kasa sun zuba ido su ga irin tasirin da dokar za ta yi wajen magance matsalar da ka iya tasowa a game da yaduwar kalaman 6atunci a kasar.
Saurari karin bayani a sauti:
Facebook Forum