Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana bukatar kudi domin nasarar yaki da zazzabin cizon sauro a Afika


Sauro da yake kawo cutar zazzabi
Sauro da yake kawo cutar zazzabi
Kungiyar hadin kan shugabannin kasashen nahiyar Afrika a yunkurin yaki da zazzabin cizon sauro tace an sami ci gaba a yunkurin yaki da cutar.

Kungiyar da ta kunshi kasashen nahiyar Afrika 43 da ake kira da turanci “African Leaders Malaria Allience” ko kuma ALMA a takaice, wadda aka kafa da nufin shawo kan mace macen da ke da ake dangantawa da zazzabin ciwon sauro, tace ta yi damarar shawo kan cutar yanzu fiye da lokutan baya.

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf wadda take jagorancin kungiyar ta bayyana a wajen wani taron koli na kungiyar hadin kan kasashen Afrika cewa, ana bukatar Karin dala biliyan uku da miliyan dubu dari biyu cikin shekaru uku masu zuwa kafin a iya shawo kan mace macen da ake yi ta dalilin zazzabin cizon sauro.

Tace, tilas ne “kason kudin ya fito daga kasashen Afrika. Ba zamu iya neman kasashen duniya su tallafa a harkokin kiwon lafiyar kasashen Afrika ba idan muma bamu kashe kudi a wannan bangaren da kanmu.”

Wani bincike da kungiyar ALMA ta gudanar kwanan nan ya nuna cewa, idan aka kashe dala daya wajen yaki da zazzabin cizon sauro a kasashen Afrika, ana samun a kalla habakar tattalin arzikin kasashen nahiyar da kimanin dala arba’in.
Membobin kungiyar sun kuma jadada bukatar kara gudummuwar da suke bayarwa tare da taimakon bankin bunkasa nahiyar Afrika da kuma babban bankin duniya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG