Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Mace Ta Farko Da Zata Rike Mukami Mafi Girma A Hong Kong


 Carrie Lam
Carrie Lam

Hong Kong ta zabi Carrie Lam ta zamo mace ta farko da zata rike mukami mafi girma a birnin, zaben da aka kareshi wanda da yawa suke wa kallon ba kare shi ta hanyar demokradiyya ba.

A baya Lam ta yiwa Hong kong aiki a matsayin Babbar sakatariyar gwamnati kuma itace ‘Yar takarar da China ta fi daga cikin 'Yan takarar da suka tsaya.

Duk da a zaben bayyana ra’ayi na al’umma Lam bata da farin jini, ta make abokanan takarar ta maza guda biyu tsohon sakataren kudi John Tsang da kuma Tsohon Alkali mai ritaya Woo Kwok-hing inda ta wawashe kuri’u 777. Gaba daya kusan kaso 70 cikin dari na kusan kuri’u 1,200 da aka kada a kwamitin zabe na birnin, kwamitin da yake makare da ‘Yan amanar Beijing.

A jawabin ta na nasarar zaben, ta ce zata maida kai ne akan Hong kong, da ta kira “Gidan mu” domin kaucewa daga hanyar China da muke akai yanzu. Ta ci alwashin gina al’umma mai inganci ta hanyar hada kan 'yan kasa da kuma share musu hawaye kan damuwarsu.

Dan rajin Demokradiyya a tsohuwar kasar da birtaniya ta taba mamayewa ya ki yarda da nasarar Lam a wannan zaben, tun da yan kasar miliyan 7 basu da izinin yin zabe haka kuma saboda Yan tsirarun mutane ne ‘yan amanar Beijing suka zabe ta.

Sun ci alwashin bijirewa gwamnatin ta idan dai har ta ajiye abinda Beijin ke bukata ta saka ra'ayin China a gaba akan birnin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG