A kowace ranar Muludi a kan yi karance karance Kur'ani da hadisansa a matakai daban daban. Wasu ma na soma wannan ranar tun makwanni biyu kafin ta zo da daukan lokaci domin yinkaratun Kur'ani mai girma. Ko jiya ma hakan ya faru a fadar mai girma Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-Kanemi.
Shehun Borno ya ce karance karancen Kur'ani da zikiri nada cikakken tarihi. Ya ce haka suka gada tun lokacin zamanin birnin Ngazagarmu zuwa Kukawa har aka kawo Borno. Biranen sun dade a duniya fiye da shekaru dubu. Kakan shehun Borno na yanzu shi ya kafa birnin Maiduguri. Tun daga lokacin da aka kafa garin a shekarar 1903 su ke yin wannan bikin da karatu har kawo yanzu.
Shugaban Zawiya Abdul Fatayi ya ce babu ranar da ta fita daraja a cikin ranakun da Allah ya halitta saboda rana ce da aka haifi wanda aka yi halittar duniya da ma duniyar dominsa. Ko daren lailatu kadari manzon Allah ne ya sa ya yi daraja amma bai fi ranar da aka haifesa ba. Wanna rana ita ce ta kawo hasken musulunci da kuma hanya mafi kyau.
A wannan rana duk Musulmi ya kamata ya yiwa manzon Allah salati a kuma tunatar da mutane halayan manzon Allah. A duba yaya Manzon Allah ya yi hulda da Musulmi da wanda ba Muslmi ba? Yaya ya zauna da makwaftansa? Yaya ya yi hulda da iyalansa? Ya ce halayan da ake nunawa mutane tamkar na musulunci ba su ba ne halayan Manzon Allah.
Ga karin bayani.