Tun farko dai an tsare tubabbun yan Boko Haram din a cibiyoyin daidaita tunaninsu dake Legas da jihar Gombe, mallakar gwamnatin tarayya. baya ga gyaran zukata da malaman addinai ke yi musu, an koya musu sana’o’i daban-daban domin su dogara da kansu bayan an mayar da su cikin al’umma.
Alhaji Bala Manu Gadau, babban sakatare a ma’aikatar addini ta jihar Bauchi, shine ya karbo tubabbun yan boko haram din ya kuma mikasu ga hannun kwamishinan harkokin addini na jihar, ya gargade su da su dauki abin da ya samesu a matsayin kaddara.
Kwamishinan ma’aikatar addini na jihar Bauchi, Alhaji Babayo Umar Kesa, ya yi jawabi a hukumance tare da fadakarwa kan su zama al’umma na gari.
Tubabbun yan Boko Haram din da aka yaye sun bayyana irin abubuwan da suka koya na rayuwa da addini da kuma wanda zasu rike don dogaro da kansu.
Iyaye da kuma yan uwan tubabbun yan Boko Haram sun bayyana jin dadinsu, kasancewar sun sake haduwa da ya’yansu bayan tswon lokaci da rabuwa.
Domin karin bayani ga rahotan Abdulwahab Muhammad.