An dai sake gurfanar da magidantan bakwai gaban babbar Kotu mai daraja ta uku, wadda ke da hurumin sauraren tuhumar da ake musu na yi wa yarinyar fyade.
Lamarin ya faru ne bara a shekarar 2020, tun farko an gurfanar da su ne gaban Kotun Majistare wadda ba ta da hurumin sauraren shari’ar, kuma daga baya aka bayar da belin su, inda lamarin ya fara tafiyar hawainiya sai bayan da mahaifiyar yarinyar ta fara koke-koke da matsa lamba sannan gwamnati ta yi alkawarin bin kadin shari'ar.
Da alamu yanzu dai gwamnati ta dauki hanyar tabbatar alwashin da ta sha domin babban lauyan gwamnati ne da kansa ya shigar da karar a gaban babbar Kotun, duk da yake tun farko wasu na tunanin tamkar mutanen da ake tuhumar sun fi karfi doka.
Su ma kungiyoyin da ke fafutukar ganin an yi wa yarinyar adalci sun nuna gamsuwa da wannan mataki, duk da ya ke a cewar Rabi'u Bello Ghandi, na kungiyar Save The Child Initiative, akwai ire-iren wannan yarinya da yawa wadanda ya kamata gwamnati ta tallafa wa.
Alkalin Kotun mai shari'a Malami Umar Dogon Daji, ya daga shari'ar zuwa ranar uku ga watan Maris lokacin da za a fara gabatar da shaidu.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.