Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsige Ministan Harkokin Wajen Pakistan


Minista Asif
Minista Asif

Wata babbar kotu a kasar Pakistan ta tsige ministan harkokin wajen kasar, ta kuma haramta mashi tsayawa takarar wata kujera a kasar kwata-kwata, saboda ya boye wasu kaddarorinsa a kasashen ketare

Hukuncin da aka yanke akan tsohon ministan harkokin waje Khawaja Asif da aka yanke yau Alhamis na zuwa ne bayan watanni tara da suka gabata da kotun kolin kasar ta yanke hukuncin tsige firayin minista Nawaz Sharif akan wani abu makamancin wannan.


Ba tare da wata jayayya ba, wani kwamitin alkalai guda uku daga babbar kotun Islamabad ya gano cewa, Asif ya aikata laifin boye cewa yana aikin kwantaragi da wani kamfani a hadaddiyar daular larabawa, kuma yana karbar albashi mai tsoka ta wani banki da bai taba bayyanawa ba.


Bisa dokar zaben Pakistan, dole ne ‘yan takara su bayyana duk kaddarorinsu na gida da na waje a takardar neman tsayawa takara kafin su cancanta tsayawa takarar zabe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG