Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shawarci Najeriya Ta Yi wa Al'umma Aiki da Kudaden Da Ta Kwato


 Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalong
Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalong

Kungiyar kwararrun 'yan jarida reshen jihar Filato ta shawarci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi amfani da kudaden da ta kwato daga wadanda suka wawuresu, ta yi wa al'umma aiki domin inganta rayuwarsu.

Shugaban kungiyar kuma tsohon kwamishanan yada labarai a jihar Filato Mr. Gideon Barde yace a matsayinsu na tsoffin 'yan jarida da suka kwashe fiye da shekaru arba'in suna aikin jarida, hakki ne a kansu su dinga bibiyar tsare-tsaren gwamnati suna kuma ba da shawarwari domin ci gaban kasa.

Ya ce a tsarin mulkin Najeriya 'yan jarida suna da aikin da kasa ta dora masu.

Ya kuma ce suna murna da shirin Shugaba Buhari na kawo hanyar da za'a kwato kudaden da mutane suka sace daga gwamnati.

Ya kara da cewa kudaden da ake kwatowa ya kamata gwamnati ta duba rayuwar 'yan kasa ta kawo masu sauyi.

Shi ma tsohon kwamishanan zabe a Najeriya Godfrey Miri ya yabawa gwamnatin tarayya wajen bankado makudan kudaden.

Sai dai ya kira ga EFCC ta ba da jimillar kudaden da ta karbo domin kowa ya sani.

A 'yan mawakkani da suka gabata ne, wata kotu a Legas ta ba gwamnati umurnin yin shelar neman masu kudaden da aka kwato har na tsawon makwanni biyu.

Idan har babu wanda ya gabata sai ta rike kudaden.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG