WASHINGTON, DC —
Fiye da sa’o’i ashirin da hudu (24) kena da aka kama wani jirigin sama me dauke da makamai da jirage masu saukar angulu, hade da wasu turawa bakwai (7) a filin saukar jirage na kasa-da-kasa na Mal. Aminu Kano a birnin Kano. Amma har yanzu a hukumance babu wani abu da ke fitowa. Don bayyana ma al'umar duniya ko wannan jirigin da kayan na wace kasa ce.
Sai dai al’umomi a garin na kano nata bayyana damuwarsu. Rahotanni na cewar wannan jirgin na kasar Rasha ne, ya yin da wasu ke cewar jirgin ya sauka a Najeriya ne don yasha mai kamin ya isa kasar Chadi, inda zai je don kai kayan.