A makon da ya wuce wasu mutane da ake zato Filani ne suka kai hari kan kauyen Rukubi a cikin karamar hukumar Doma jihar Nasarawa. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da ma asarar dukiyoyi.
A wani taron neman zaman lafiya da sarakunan karamar hukumar suka yi a fadar Andoma na Doma Alhaji Ahmadu Aliyu Onanu da alama an samo bakin zaren rikicin. Sarakuna biyu ke rigima da junansu, wato sarkin Agbashi da sarkin Akpanaja. Sarakunan sun yafe ma juna kuma sun dauki alkawarin zaman lafiya da al'umominsu.
Andoma Alhaji Ahmadu Aliyu Onanu shi ya babbatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron da aka yi a fadarsa wanda ya samu halartar wakilin gwamnatin jihar Alhaji Abdulhamid Yakubu Kwara da Kwamishanan 'Yan Sandar jihar Alhaji Umar Shehu da ma wasu masu fada a ji cikin jihar.
Ga karin rahoton da wakiliyarmu Zainab Babaji ta aiko.