Wata majiya da ba ta gwamnati ba ta tabbatar da mutuwar mutane kimanin uku a zanga zangar da aka gudanar a birnin Niaamey fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, biyo bayan mummunar tarzoma da aka yi da aka kona majami’u da dama da kuma wadansu cibiyoyin gwamnati.
Masu zanga zangar dai suna nuna fushinsu ne dangane da zanen batancin da aka yiwa annabi Muhammadu SWA da mujallar barkwancin nan ta kasar Faransa Charlie Hebdo tayi, bayan harin ta’addancin da aka kai mata da aka kashe ma’aikatanta goma sha biyu.
A cikin hirarshi da Sashen Hausa wani malamin makaranta da aka yi abin a ganin idonsa, Issoufou Mamane Moutari ya bayyana cewa, hukumomi sun kama Limaman Musulmi da dama dangane da tashin hankalin kafin daga baya aka sakesu.
Bisa ga cewarshi an kona majami’un kirista da dama yayin tarzomar. Ya kuma ce I zuwa lokacin hira da Sashen Hausa ,kura ta fara lafawa, yayinda kuma aka girke jami’an tsaro a muhimman wurare, duk da haka yace ana zama zullumi, da gudun kada lamarin ya sake aukuwa.
Ga cikakkiyar hirar.