Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Zabar Adefunke Adeyemi A Matsayin Shugaban AFCAC


An sake zaben Adefunke Adeyemi a matsayin babbar sakatariya a hukumar kula da sufurin jiragen saman Afirka (AFCAC) a yayin karo na 35 na babban taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a birnin Brazzaville, na Congo.

Mashawarci na musamman a kan harkokin yada labarai ga ministan sufurin jiragen sama, Tunde Moshood, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a yau Alhamis.

A cewarsa, ministan sufurin jiragen da bunkasa zirga-zirgar sararirin samaniya, Festus Keyamo, ya halarci taron da ke gudana a kasar Congo Brazzaville kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen sake zabarta.

Moshood ya kara da cewa ministan ya jagoranci muhimmiyar tattaunawar diflomasiya da mambobin kungiyar hada kan Afrika ta AU, inda ya nemawa takarar Adeyemi goyon baya.

“Wannan nasara ba ta takaita ga Najeriya ba kawai illa nasara ce ga ilahirin harkar sufurin jiragen saman nahiyar Afirka,” a cewar keyamo jim kadan bayan zaben.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG