Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Rantsar da Umar Al-Bashir a Matsayin Shugaban Sudan


Shugaba Umar Al-Bashir na yayinda aka rantsar dashi
Shugaba Umar Al-Bashir na yayinda aka rantsar dashi

Bayan ya yi shekaru 26 yana mulki shugaban kasar Sudan Umar Al-Bashir ya sake samun karin wa'adin shekaru biyar

Shugaban kasar Sudan Umar Albashir wanda kotun kasa da kasa dake birnin Hugue ke nema akan laifin yaki, an sake rantsad dashi a matsayin sabon shugaban kasar a jiya Talata.

Al-Bashir zai sake kwashe wasu shekaru 5 a matsayin shugaban kasar ta Sudan. Yayi alkawarin zai yaki cin hanci da rashawa kana ya inganta tattalin arzikin kasar sailin ya dawo da zaman lafiya a yammacin kasar.

Haka kuma yayi alkawarin samar da zaman lafiya a sassan kasar uku masu kokarin ganin sun kifar da gwamnatin sa da suka hada da yankin Dafur, Kordofan da kuma yankin kogin Nilu.

Shugaba Al-bashir ya jaddada ahuwa ta dindindin ga dukkan dan tawayen da ya ajiye makaminsa domin shiga sulhu.

Shi dai Al-Bashir yamulki sudan har na tsawon shekaru 26, wadda yaki bai dai daita ta ba sai dai kam tasha yawan takunkunmi daga kasashen duniya a lokutta daban-daban, wanda har hakan yasa tayi babban hasarar samun kudin shiga na kasuwancin mai

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG