WASHINGTON D.C. —
Hukumomi a Najeriya na bikin tunawa da ranar Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar sake bude ofishin majalisar a hukumance a Abuja, babban birnin kasar.
Tun a shekarar 2011 aka rufe ofishin, bayan wani mummunan hari da mayakan Boko Haram suka kai ginin.
An bude ofishin ne a jiya Alhamis, shekaru takwas bayan da wani dan kunar bakin wake ya kutsa da mota cikin ginin, ya ta da bam.
A cewar karamin Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da fannin ayyukan jin-kai, Mark Lowcock, sake bude ofishin, wata alama ce da ke nuna cewa ba za a mika-wuya ga masu ayyukan ta’addanci ba, yana mai cewa, za su ci gaba da taimakawa Najeiriya wajen cin ma burinta na ganin ta samu makoma mai kyau da cikakken tsaro.