An rantsar da Mohammed Morsi a matsayin shugaban Masar, hakan ya bude sabon babi a tarihin kasar wacce ta zabi farar hula na farko ya jagoranci kasar.
Yau Asabar Mr. Morsi yayi rantsuwar kama aiki a wani biki da aka yi a aharabar kotun tsarin mulkin kasar. Yayi alwashin mutunta tsarin mulkin kasar.
Sabon shugaban ya gaji tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak, wadda boren ya jama’a ya hambarar da shin daga kan mulki.
Ana sa ran sabon shugaban kasar zaiyi jawabi ga al’umar kasar wani lokaci a wunin yau.
Bikin rantsar da shi yazo ne kwana daya bayan da yayi jawabi ga dubub dubatan magoya bayn sa wadanda suka cika dandalin Tahiri a zanga zangar da suke yi ga majalisar mulkin sojan kasar. Ya jinjinawa misrawa a duk fadin kasar haer da wadan da suke ketare, yan main cewa jinin ‘yan juyin juya hali da wadanda suka jikkata sune suka share hanyar samun ‘yanci cikin kasar. Haka kuma yace yana mai matukar kaunar wan nan babbar karramawar da jama’ar kasar suka yi masa.
Tund a farko sabon shugaban aksar yace a gaban majalisar dokokin kasar zai yi rantsuwar kama aiki. Amma majalisar mulkin sojin kasar tace tilas a ranatsar da shi gaban kotun tsarin mulki, domin an rusa majalisar dokokin kasar wacce galibi ana ganin wadan da suka cike majalisar ‘yan gani kashenin addini ne.
Masu nazarin al’amauran yau da kullum suka ce sai tayu wan nan ne sa- in-sa na farko a kokarin nuna iko tsakanin sojoji da sabon shugaban kasar na Masar.