Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kwashe mutane 6,000 daga tsibiran Vanuatu a saboda barazanar amon wuta


Amon wuta
Amon wuta

Hukumomi a Vanuatu sun kwashe mutanen dubu shidda daga gidajensu a saboda barazanar amon wuta daga tsaunin Manaro dake tsibirin Ambae

Hukumomi a Vanuatu sun kwashe mutanen da yawansu ya kai dubu shidda daga gidajensu zuwa sansanonin gaggawa da aka kafa a saboda barazanar amon wuta daga tsaunin Manaro dake tsibirin Ambae.

Tsaunin na Manaro a tsibirin Ambae yayi makonin yana tumbudin toka da wuta da kuma tururin iskar gas da aka danganta da amon wuta, al’amarin daya tada tsoron akwai yiwuwar tsaunin zai yi amon wuta.

A shekara ta dubu biyu da biyar tsaunin yayi amon wuta na karshe.

Kimamin mutane dubu maitan da tamanin ne suke zaune a tsibirai tamanin dake warwatse a Vanuatu dake yankin Pacific. Kuma tsibiran suna yankin da aka lakawa suna da’irar wuta, ko kuma Ring of Fire da turanci inda girgizar kasa da amon wuta abubuwa ne da aka saba gani a yankin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG