Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwantar Da Nelson Mandela A Asibiti


Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela
Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela
An kwantar da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela a asibitin birnin Pretoria.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar Jacob Zuma tace an kwantar da tsohon shugaban kaasr dan shekaru 94 ne a asibiti jiya domin gudanar da wadansu gwaje gwaje da yake bukata sabili da tsufarsa. Sanarwa ta ce babu wani abin damuwa.

Karfin Mr. Mandela ya ragu ainun kuma bai fita bainin jama’a ba cikin shekaru da dama.
An kwantar da shi a asibiti cikin watan Fabrairu sakamakon ciwon mara.

Mr. Mandela ya zama shugaban Afirka ta kudu bakar fata na farko a shekara ta dubu da dari tara da casa’in da hudu. Kafin ya zama shugaban kasa, ya shafe shekaru ishirin da biyar a gidan yari sabili da yaki da wariyar launin fata.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG