Shugaban kasar Kamaru ya ce an kubutar da wasu mutane 27 da wasu mayakan da ake zargi 'yan Boko Haram ne ke yin garkuwa da su bayan sun kama su afarkon shekarar nan, a cikin mutanen har da 'yan kasa China 10 masu aiki a kasar ta Kamaru.
Shugaba Paul Biya ya fada a yau Asabar cikin wata sanarwa cewa mutanen sabbin kubutarwa wadanda suka hada har da matar mataimakin firai ministan kasar Kamaru, su na nan lafiya.
Mr.Biya ya ce mutanen wadanda aka kama a cikin watannin Mayu da Yuni a garuruwanWaza da kuma Kilofata, an mika su ga hukumomin kasar Kamaru.
Kasar Kamaru ta hada kan iyaka mai tsawo da kasar Najeriya inda 'yan Boko Haram ke mummunan boren zubda jini tun shekarar 2009.
Kungiyar aka dorawa laifin kisan dubban mutane a fadin yankin arewacin Najeriya, kuma ita ce ta dauki alhakin sace 'yan mata fiye da 200 daga garin Chibok a cikin watan Afrilu, al'amarin da ya hasala kasashen duniya.
Har yanzu gwamnatin kasar Najeriya na faman neman kawo karshen hare-haren, duk kuwa da dubban sojojin da ta zuba a arewa maso gabashin kasar tare da kafa dokar ta baci a jahohi uku da suka hada da Borno, da Yobe da Adamawa.