Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kubutar Da Matar Da Aka Kulle A Daki Kusan Shekaru Biyu A Rigasa


Wata mata ‘yar Najeriya wanda dan'uwanta ya kulle ta a cikin wani daki mai duhu kusan shekaru biyu, ta sake samun ‘yancinta.

Bayanai na nuni da cewa, dan' uwan Hassana Sale wadda take da yara hudu ya kulle ta ne saboda kada ta koma gidan mijinta.

Wata kungiya mai zaman kanta a Kaduna da ake kira Gidauniyar Arida Relief da ta ceto Hassana, ta ce an same ta a cikin "mummunan yanayi" a kulle a cikin daki a yankin Rigasa a Kaduna. Shugabar kungiyar, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana wa Muryar Amurka, yadda akayi suka ceto Hassana Sale a yankin Rigasa, inda ta bayyana cewa dan uwan Hasssana mai suna Lawal Sale ya kulle ta a daki mai duhu sabili da niyyarta na komawa gidan mijinta.

Ta kuma bayyana cewa, masu taimako su suka kawo musu labarin Hassana Sale cikin sirri.

A hirarshi da Muryar Amurka, wani dan'uwanta mai suna Komarat Adamu Sale ya ce, Hassana kanwar sa ce, kuma ta samu matsalar tabuwar hankali bayan ta rabu da mijinta, dalili ke nan da suka yanke shawara a ajiye a daki, sai dai bai san yanyain da aka kulle ta ba..

Shima tsohon mijin nata Muhammad Fada ya yiwa Muryar Amurka Karin haske akan lamarin, inda ya ce, Hassana ta samu matsalar tabin hankali ne shi yasa suka rabu, ya kuma musanta cewa yana dukanta.

Kwamishiniyar mata da walwalar Al’uma ta jihar Kaduna, Hajiya Maryam Baba ta bayyana cewa, an kai Hassana asibiti, kuma suna nan suna bincike.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isah Lawal Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:06 0:00
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG