‘Yan sandan Kenya sun ce an kashe mutum guda, aka sace ma’aikatan agaji hudu ‘yan kasashen waje a makeken sansanin ‘yan gudun hijira na Dadaab dake kusa da bakin iyakar kasar da Somaliya.
Kwamishinan gunduma na Dadaab, Albert Kimathi, ya fadawa VOA a jiya jumma’a cewa wannan al’amari ya faru a wani yankin sansanin da ake kira Ifo Camp 2, a gidan wata kungiyar agaji ta kasar Norway. Yace wanda aka kashe dan kasar Kenya ne, yayin da aka sace mutum guda daga kowace daya daga cikin kasashen Norway, Colombia, pakistan da kuma Philippines.
Kimathi ya ki ya ce uffan game da ko su wanene ake kyautata zaton sun kai harin na jiya jumma’a.
Sakatare-janar ta kungiyar agajin ta kasar Norway, Elisabeth Rasmussen, wadda ke tafiya cikin wannan kwambar motocin agaji a lokacin da aka kai musu farmaki, ta ce su na cikin wani yankin sansanin ne da ake dauka cewa ba ya tattare da hatsari.
Ta ce mutane kimanin hudu da kananan bindigogi ne suka kai musu farmaki. Sun yi ta harbe-harbe, suka kuma kwace mota guda.
Hukumomin kenya sun dora laifin sace-sacen mutane da aka yi a can baya a sansanin Dadaab da kuma yankunan dake kusa da bakin iyakar a kan kungiyar tsagera ta al-Shabab.
Kenya ta kafa hujja da sace-sacen mutanen a zaman dalilinta na tura sojoji cikin Somaliya domin yakar al-Shabab a watan Oktobar bara. Kungiyar ta musanta satar mutane a kasar Kenya.