Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Diyar Dan Majalisar Borno


Jana'izar marigayiyar
Jana'izar marigayiyar

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe diyar dan majalisa jihar Borno da ke wakiltar mazabar Ngala, Bukar Abacha a gidanta da ke birnin Maiduguri a yammacin ranar Talata.

A cewar rahotanni daga kafafen yada labaran kasar, mijin matar da aka kashe mai suna Fatima Alhaji Bukar ne ya ga gawar matarsa a gidansu an daure hannuwanta da kafafunta, yayin da danta dan shekara biyu ke kuka a gefe guda. Daga nan ya dauki gawar ya kai ta ofishin 'yan sanda.

Faruwar wannan lamari dai ya haifar da tashin hankali a tsakanin al’ummar yankin, inda suka yi ta tururuwa zuwa wajen don gane wa idonsu abin da ke faruwa.

Rundunar ’yan sandan Gwange da ke birnin Maiduguri ta dauki gawar matar zuwa Asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri domin gudanar da bincike.

Wannan dai na zuwa ne biyon bayan umarnin da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya ba hukumomi a kan su mayar da gawar asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri domin a yi bincike.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama Adam Alhaji Ibrahim mijin Fatima, a cewar jaridar Leadership.

Wata majiya daga bangaren iyalin marigayiyar ta ce an kama Adam ne a daren ranar Talata, 17 ga watan Oktoban 2023.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG