Yayin da Lily Botsyoe take karatun kimiyar komputa a wata jami’a a Ghana, dalibai suna rubutu a kan farin allo saboda basu da isassun komputa da zasu yi nazari dasu. Wanna lamari yasa kwarewar dalibai wurin tsara lambobi ya yi matukar wahala, tace wannan al’amari ya ci gaba har izuwa wannan lokaci.
Tace muna da dalibai da suke gama karatu suna da ilimin komputa a kan takarda, kuma hakan yana da kyau, saboda bai yiwuwa mutum ya gane aiki da komputa har sai ya samu iliminsa a kan takarda. Amma kuma wannan lamari yasa masana’antu basu samun kwararru ma’aikata da suka san amfani da komputa tun wurin karatu, inji Botsyoe.
Tace tana so taga ana baiwa dalibai kayan aiki, musamman ‘yan mata da manyan mata saboda su samu cikakken kwarewar fasaha a Ghana da ma sauran sassan Afrika.
A Yau, sunan Botsyoe ta zama wani tsari gwaji da kuma aiki na koyi da matan da suka yi fice a fanni tsara lambobi da kirkiran bayanan wucin gadi.
An dai gabatar da Botsyoe a taron bukin makon mata a fannin fasaha a Accra da abokiyar aikinta kwararriya a kimiyar tattara bayanai, Aseda Addai-Deseh.