Taron da aka yi a birnin Gombe ya sa gwamnonin shiyar sun daura damarar shawo kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a jihohinsu. Gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya ce lokaci ya yi da zasu fuskanci abubuwan dake gabansu wadanda suka kunshi samar ma matasa guraben aiki da kuma tabbatar da cewa an samu zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin shiyar.Ya ce sun hada karfi da karfe domin su cimma nasara kan duk abubuwan da suka addabesu. Ya ce ya zama wajibi su yi aiki tukuru har sai sun cimma nasara.
Shi kuma gwamnan jihar Gombe mai masaukin baki Ibrahim Hassan Dankwambo cewa ya yi su gwamnonin shida sun zauna sun yi nazari bisa ga abubuwan dake faruwa a kasar musamman shiyarsu cewa ya kamata su zauna su gyara gidansu. Idan basu gyara gidansu ba babu wanda zai zo ya taimakesu. Ya ce a taron sun ce kowa ya ajiye ban-bancin siyasa domin talauci bai damu da jam'iyyarka ba. Haka ma mutuiwa bata daukan dan jam'iyya daya ta bar wani dan wata jam'iyyar. Ya ce wannan takai-takai ne zasu yi.
Mukaddashin gwamnan jihar Taraba Alhaji Garba Umar ya ce sun fadada hanyar zuba jari a yankunan nasu. Ya ce kamar yadda ya fada a taron sun nemi wadanda zasu zo su zuba jari kuma zasu taimakawa ire-iren wadan nan.
A wata sabuwa kuma yariman Kashere Alhaji Habu Muazu ya mayar da martani ga sarkin Gombe dangane da bukatar da ya mikawa shugaban kasa da ya dage Jami'ar Kashere zuwa cikin garin Gombe. Ya ce bukatar bata dace ba sam kuma basu ji dadi ba. Ya ce kai Jami'ar Kashere zai taimaki 'yan makarantar su dage su yi karatu ba tare da shiga wasu abubuwa ba. Ya ce tsakanin Kashere da Gombe tafiyar minti talatin ne kawai kuma garin nada wuta da hanyar mota da ruwa ga kuma filin Allah ta'ala ba sai an biya wani kudin diya ba.
Abdulwahab Mohammed nada rahoto.