'Yan Sanda a Zimbabwe sun kama ma'aikatan jinya 12 wadanda suka fito zanga-zanga a wajen asibitocin gwamnati.
Kungiyar ma;aikatan jinya ta kasar ta ce sun fito zanga-zanga ne domin bukatar a biya su albashi da kudin dalar Amurka yayin da hauhawar farashin dala ke yi wa albashinsu illa.
Wani ma'aikacin Reuters ya shaida yadda 'yan sanda a birnin Harare suka kama wasu ma'aikatan. Mai magana da yawun 'yan sanda a kasar, Paul Nyathi ya ce bai da masaniya kan lamarin.
Ma'aikatan wadanda suka fito rike da kwalayen da aka rubuta "babu dala, babu aiki" da kuma "ma'aikata basa iya numfashi" sun ce sun fito zanga-zanga ne saboda bayyana yadda ba za su iya rayuwa da albashin dalar Zimbabwe 3000 ba.
A cewar wata mata a wurin zanga-zangar, "ba zan zauna ina aikin banza ba, dole sai na ci abinci saboda in iya yin aiki na da kyau."
Zanga-zangar wacce ta faru a wurare daban-daban, ciki har da asibitin Zimbabwe mafi girma da ke birnin Harare, na faruwa ne a lokacin da Covid-19 ke kara kama mutane a kasar.
Ya zuwa yanzu dai mutane akalla 716 ne ke fama da cutar, yayin da takwas suka rasa rayukansu.
Facebook Forum