Kimanin kilo 240 na tabar wiwi da aka nade a sinki-sinki ne hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato OCRTIS ta kama a hannun wasu diloli wadanda dubunsu ta cika bayan da ‘yan sanda suka gudanar da binciken kwakwaf a watan babbar motar daikon kaya
Mataimakiyar darektan hulda da jama’a a hukumar ‘yan sanda ta kasa kwamishiniya Nana Aichatou Ousmane Bako ta yi wa Muryar Amurka karin bayani a lokacin da aka gabatar da wadanan diloli a gaban manema labarai.
“Kwayar da suke dauke da ita sai da ta ketare wajen kasa uku kafin aka gano su a yanzu.”
A cewar Bako “sai wanda ya san aikinsa zai iya gane wadannan kwayoyin bisa yadda suka boyesu.”
Babban alkali mai tuhuma Procureur de la Republique da mukarrabansa sun ziyarci ofishin hukumar ta OCRITIS domin jinjinawa ma’aikata sakamakon gamsuwa da nasarorin da suke samu.
“Safarar miyagun kwayoyi haramtaciyar sana’a ce da duniya ta tanadi hukunci mai tsanani akan duk wanda ya jefa kansa cikin wannan danyen aiki” inji Procureur Maman Tsayabou Issa.
Ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin a yanke musu hukuncin da ya dace da su.
Bayan wannan lamarin, hukumar ‘yan sanda ta sake nanata kira ga al’umar Nijar akan bukatar bada hadin kai don ganin an murkushe wannan al’amari da ke ci gaba da biijirowa a kasar.
Facebook Forum