WASHINGTON D C —
Akalla mutane 49 suka rasa rayukansu, wasu fiye da 20 kuma suka sami raunuka a cikin harbe-harben da aka yi a wasu masallatan Jumma’a guda biyu na kasar New Zealand a yau.
Yanzu haka an cafke wasu mutane uku maza da mace daya dangane da harin, koda yake Firayin-ministar New Zealand, Jacinda Arden, ta ce daga cikin mutanen, ba wanda sunansa ke cikin jerin sunayen mutanen da ma’aikatun tsaro ke maida hankali a kansu.
Tuni aka riga aka tuhumi daya daga cikin mutanen, wani dan shekaru 28 da haihuwa da laifin kisan kai, kuma gobe Asabar ake sa ran gabatar da shi a gaban hukuma, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda Mike Bush ya bayyana.
Facebook Forum