Jami’ai a kasar Iraq sun ce hare haren da aka kai a wurare dabam dabam a kasar yau Lahadi ya yi sanadin kashe mutane 17 da dama kuma suka jikkata.
Hari mafi muni shine harin boma bomai da aka kai kan wadansu motoci uku a Taji, arewacin Bagadaza. Jami’ai suka ce mutane takwas sun mutu a harin sama da 20 kuma suka ji raunuka.
Wani dan kunar bakin wake kuma a Kut dake kudancin Bagadaza, ya kashe a kalla jami’an ‘yan sanda uku ya kuma raunata wadansu da dama. A Balad Ruz arewa maso gabashin babban birnin kasar kuma, wani harin bom da aka kai ya kashe ‘yan sanda biyu. An kuma kai hare hare a wadansu garuruwa.
Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin hare haren da aka kai yau Lahadi