Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kari hari a jihohin Bauchi da Gombe yayin da ake gudanar da zabe.
An kai harin na Bauchi ne a wani kauye da ake kira Yautare da ke karamar hukumar Darazo wanda ke kan iyaka da jihar Gombe.
Wakilinmu Muryar Amurka ya ce harin na jihar Gombe an kai shi ne a garin Bajoga.
A Yautare wasu mahara a cikin motoci 6 kirar Pick Up da Babura suka kari harin a wata mazaba da ke wata makarantar firamare inda suka kune ta baki daya.
Wasu mazauna yankin da wakilinmu ya tattauna da su sun ce jami’an zabe da masu kada kuri’a sun arce a lokacin harin yayin da babu tabbacin ko mutane nawa ne suka jikkata.
Shi kuwa harin na Bauchi wasu mutane ne sanye da kayan sojoji suka kai shi inda daga baya suka tsere zuwa cikin Gombe.
Babu dai bayanin da ke nuna cewa maharan na da alaka da na Gombe yayin da hukumomin jihohin suma basu ce uffan game da hakan ba.
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da bam ya tashi a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin kasar ta Najeriya.
Yau ne dai Najeriyar ke gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, zaben da ke tare da babban kalubale ga kasar yayin da jam'iya mai mulki ta PDP ke fuskantar barazanar daga jam'iyar adawa ta APC.